A wannan shiri na musamman mun karbi bakuncin Alh. Engineer Aminu Al-Amin Salisu, da kuma Dr. Bashir Ahmad Safio. Mun kuma tattauna akan tafiyar neman aure a wannan zamani, a inda bakin namu sukayi tsokaci akan matsaloli da ake fuskanta tare da bada shawarwari domin a samu mafita. A kasance tare damu cikin shirin domin jin tsokaci da shawarwari da bakon namu ya bayar.
A zango na daya na sabon shirin Mu Gudu Tare Mu Tsira Tare mun gayyato Dr. Bashir Ahmad Safiyo. Mun tattauna akan batun neman nakai a tsakanin matasa, a inda Dr. Bashir Ahmad Safiyo yayi bayanai tare bada shawarwari masu matukar amfani.