Send us a text A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar. A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane...
Show more...