Home
Categories
EXPLORE
True Crime
Comedy
Business
Society & Culture
History
Sports
Health & Fitness
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
00:00 / 00:00
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts122/v4/0b/c0/37/0bc037f6-00fc-95d9-5105-e63559438f8c/mza_11129557636118003328.jpg/600x600bb.jpg
Al'adun Gargajiya
RFI Hausa
24 episodes
19 hours ago

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Show more...
News
RSS
All content for Al'adun Gargajiya is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Show more...
News
Episodes (20/24)
Al'adun Gargajiya
Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban.
Show more...
2 days ago
10 minutes 1 second

Al'adun Gargajiya
Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa.
Show more...
1 week ago
10 minutes 30 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar
Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya domin kafa ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. Bikin na bana ya samu halattar ƙabilun Fulani da na Abzinawa da Larabawa a Nijar ɗin da wasu daga Najeriya, da Mali da burkina Faso da kuma Aljeriya.
Show more...
2 weeks ago
9 minutes 38 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa
Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni.
Show more...
3 weeks ago
10 minutes 3 seconds

Al'adun Gargajiya
Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo.
Show more...
1 month ago
10 minutes 3 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta
Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen.
Show more...
1 month ago
10 minutes 2 seconds

Al'adun Gargajiya
Sannu a hankali sana'ar ƙira na shuɗewa a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar.
Show more...
1 month ago
9 minutes 48 seconds

Al'adun Gargajiya
Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.
Show more...
2 months ago
9 minutes 59 seconds

Al'adun Gargajiya
Bikin cika shekaru 10 da faro bikin ranar Hausa ta duniya
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya tattauna ne a kan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.
Show more...
2 months ago
10 minutes 7 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda ƴan Ƙabilar Zarma ko Zabarmawa suka yi baja kolin al'adunsu a Ghana
Shirin al'adun gargajiya na wannan makon tare da Abdoulaye Issa  ya yada zango ne a Ghana, inda a ‘yan kwanakin da suka gabata, ‘Yan Ƙabilar Zarma ko kuma Zabarmawa suka yi taron baja kolin al'adunsu karo na huɗu a ƙasar.
Show more...
2 months ago
9 minutes 49 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda zamani ke tasiri akan salon magana a tsakanin al'ummar Hausawa
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda zamani ke tasiri kan salon magana ko 'Gagara Gwari' a tsakanin al'ummar Hausawa, musamman ma matasa. Masana wannan harshe da dattawa cikin al'ummar sun yi fashin baki akan dalilan da suka sanya wannan salo na zance wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa, da gudummawar da kowane ɓangare ke bayarwa wajen wannan matsalar.
Show more...
2 months ago
10 minutes 10 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda ƙabilar Tangale dake Bombe a Najeriya suka gudanar da bikin shekara-shekara
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne aka wata al'adar al'umar Tangale dake jihar Gomben Najeriya wacce a shekara ke haɗo kan ɗaukacin al'uma na ciki da wajen ƙasar. A alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
Show more...
3 months ago
10 minutes 26 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda al'adar bikin cika ciki ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa
Shirin na wannan mako ya yi duba ne kan al'adar nan da ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa, wato Sallar cika ciki da ake gudanarwa bayan Sallar layya.
Show more...
3 months ago
10 minutes 18 seconds

Al'adun Gargajiya
Tasirin al'adar ''Mai suna'' ko Takwara ga ƙabilar Kanuri a Jamhuriyyar Nijar
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan guda cikin al'adun Ƙabilar Kanuri can a kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, Al'adar da ake yiwa laƙabi da ''Mai suna'', al'adar da ke da matuƙar tasiri a cikin wannan ƙabila da ke da matuƙar yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.
Show more...
3 months ago
10 minutes 25 seconds

Al'adun Gargajiya
Tasirin rubuce-rubuce wajen alkinta al'adun gargajiya
Shirin al'adun mu na gado na wannan rana ya mayar da hankali kan gudunmowar marubuta wajen adana gargaji da tsrain al'adu
Show more...
4 months ago
10 minutes 1 second

Al'adun Gargajiya
Yadda aka gudanar da bikin al'adun Dukkawa
Shirin al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali  a kan bikin al'adun Dukkawa na wanan shekara ta 2025  wanda ya gudana a jihar Neja da ke Tarayya Najeriya.
Show more...
4 months ago
9 minutes 45 seconds

Al'adun Gargajiya
Nazarin masana kan banbancin da ke tsakanin Maita da kuma Kambun Baka
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan karon ya tattauna ne a kan Maita da kuma Kambun Baka, domin fahimtar banbancinsu a bisa bayanan masana a ɓangaren al’ada da kuma Addini. Wasu na ɗaukar maita a matsayin tsubbu inda a lokuta da dama su kan gadar wa ƴaƴansu. Sai dai kuma wasu masanan, na cewa maita baiwa ce da Allah ya yi ma wasu daga cikin bayinsa musamman domin bayar da magani ga marasa lafiya.
Show more...
4 months ago
10 minutes 3 seconds

Al'adun Gargajiya
Yadda zamani ke tasiri kan salon magana a tsakanin al'umar Hausawa
Wannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
Show more...
5 months ago
10 minutes 10 seconds

Al'adun Gargajiya
Shin wa yafi buwaya da kuma kwarewa a waƙa tsakanin Shata da Rarara
Shirin al'adun mu na Gado na wannan mako zai Dora kan ci gaban Muhawara a tsakanin Masana kan kwarewar waƙa a tsakanin mawaki Shata da kuma Rarara
Show more...
5 months ago
10 minutes

Al'adun Gargajiya
Muhawwara akan bambamci da kamanceceniya tsakanin Shata da Rarara
Shirin al’adu na wannan makon ya waiwayi al’adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban. 
Show more...
5 months ago
9 minutes 59 seconds

Al'adun Gargajiya

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.