All content for Tambaya da Amsa is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers
with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsara tambaya akan abinda ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin da ya kamata abi wajen magance matsalar.
Shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsa tambayoyin da ke neman karin bayani akan inda tsakiyar Najeriya ya kasance, da tambayar da ke neman sanin Nahiyoyi nawa ne a duniya kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa sannan wacce ta fi yawan mutane? da kuma tambayar da ke cewa, don Allah ku tambaya mana masana tattalin arziki akan mece ce TIN number kuma ina ake samunta sannan mene ne aikinta a Najeriya?
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da cigaban amsar tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa, da kuma cigaban amsar tambayar da aka yi game da cutar daji mafitsara... Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon.
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa.. Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon.
Ko menene harajin kashi 5 da gwamnatin Najeriya ke son ƙarawa akan kuɗin man fetur ga duk mai bukata?, Ku tambaya mana masana harkokin tsaro domin su yi mana bayani akan mene ne ma'anar ƴansandan jihohi da ake ta muhawara a kai a Najeriya, kuma shin yin hakan zai haifar da ɗa mai ido? wasu cikin tambayoyin masu sauraro kenan da shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ke ɗauke da amsoshinsu tare da Nasiru Sani....
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, masana sun amsa tambayoyi game da abubuwan da ke tsaida wa Mata haihuwa da Sahihancin Ingantaccen Iri da ake samarwa wato GMO a turance, sai kuma illar da gyatsar magwas ke ita ga mai yin ta.
A cikin shirin Tambaya da amsa na wannan mako,Nasiru Sani ya mika tambayoyi masu saurare ga masana,daga cikin tambayoyi da aka aiko ,mai saurare ya bukaci karin haske dangane da batun rufe sararin samaniya.
A yi saurare lafiya.................
Shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan makon ya na wannan makon tare da Nasiru Sani ya amsa tambayoyi da dama da suka hada da wada ke neman sanin dalilin kafa Hukumar Raya yankin Arewa Maso Yammcin Najeriya.
A yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da ci gaban tattaunawa da Dr. abdulmumini Shehu Makarfi daga jihar kaduna akan shakkuwa da jarirai ke fama da ita.
Kamar yadda aka saba, a wannan karon ma shirin 'Tambaya da Amsa' ya lalubo wa masu sauraro amsoshin wasu daga cikin bayanan da suka nema daga masana fannin da suka yi tambaya a kai.
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya tattauna cigaban amsar masu tambaya a kan cutar nan ta karkarwar jiki da ake kira Parkinsons a turance.
Shirin Tambaya Da Amsa ya amsa wasu daga cikin tambayoyinku, ciki harda bayanai kan cutar nan ta karkarwa wacce a turance ake kira Parkinson, haka nan shirin ya kuma amsa tambaya dangane da abinda yake sanyawa jira-jirai yawan shaƙuwa da kuma irin illar da ke musu.
Bukatar sanin irin rawar da masarautar Bachi ta taka a lokacin jihadin Usman Danfodio.
Akan wannan tambaya ce wakilimmu na jihar Bauchi ya zanta da Alhaji Ado Garba Dan-rimi, Wakilin Tarihin Bauchi kuma Shugaban Cibiyar Nazarin Tarihi ta Masarautar Bauchi.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan ko da gaske ne akan rufe sararin samaniya ta hanyar hana jirage wucewa ta sararin samaniyar wata ƙasa?
A yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da kawo muku bayanai ne kan dalilan da suka sanya shugaba Tinubu na Najeriya ya hakikance sai an yi gyaran dokokin haraji a kasar wanda gashi har an kaiga yasa hannu ta zama doka.
A yau shirin tamabaya da amsa, tare da Nasiru Sani, zai kawo muku bayanai ne akan tasirin tsarin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙabawa ƙasashen Canada da Mexico da kuma China akan ƙasashe Afirka.
Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan rana tareda Nasiru Sani, cigaba ne na tarihin Sarkin Musulmi Muhammed Bello da kuma wasu karin tambayoyi na masu sauraro suka aiko mana.