Home
Categories
EXPLORE
True Crime
Comedy
Society & Culture
Business
Sports
Health & Fitness
Technology
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
Loading...
0:00 / 0:00
Podjoint Logo
US
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts112/v4/6a/3e/a9/6a3ea9d9-42ce-f7b7-350a-71e1051dc59b/mza_13919166392056779798.jpg/600x600bb.jpg
Muhallinka Rayuwarka
RFI Hausa
24 episodes
17 hours ago

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

Show more...
News
RSS
All content for Muhallinka Rayuwarka is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

Show more...
News
Episodes (20/24)
Muhallinka Rayuwarka
Barazanar wutar daji da ke lakume gonakai a Jamhuriyar Nijar
A cikin wannan shirin ,za mu leko Jamhuriyar Nijar inda a duk shekara ake fuskantar barazanar wutar daji da ke lakume gonakai da cimaka. Hukumomin Nijar sun dau matakai domin kawo karshen  wannan al'amari da manoma da kuma jama'a ke kuka  a kai.
Show more...
1 day ago
20 minutes 1 second

Muhallinka Rayuwarka
Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya
Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba.
Show more...
1 week ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Masana game da fallen da ke bai wa ɗan Adam kariya daga sinadaran hasken rana
A wannan makon, shirin zai mayar da hankali ne akan wani rahoton da masana suka fitar, wanda ke nuna cewa fallen nan ko shimfidar da ke bai wa ɗan Adam kariya daga wasu sinadaran hasken rana masu haɗari, da ake kira Ozone Layer, wanda kafin yanzu ake bayyana damuwa a game da lalacewar da ya fara yi, sakamakon ayyukan da ɗan Adam ke aiwatarwa ya fara gyaruwa. Sai ku biyo mu domin za mu tattaunawa da masana, shehunnan malamai akan wannan maudu’i.
Show more...
2 weeks ago
20 minutes 29 seconds

Muhallinka Rayuwarka
Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam.
Show more...
3 weeks ago
19 minutes 2 seconds

Muhallinka Rayuwarka
Yadda manoma a Jahuriyar Nijar suka koma noman Gyaɗa da Gujiya gadan-gadan
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda manoma a Nijar suka koma noman Gyaɗa da riɗi gadan-gadan bayan sun yi watsi da shi tsawon shekaru, saboda matsaloli da noman ke fuskanta.Maraɗi ce kan gaba a noma Gyada ko Gujiya shekaru aru aru, sai Zinder da kuma Doso, waɗanda suka taimaka wajan hada-hadar kasuwancin Gyaɗa har a Kano inda ake tattara Dalar Gyadar.Yawan noman Gyadar ne ma ya sa turawan mulkin mallaka suka kafa masana’antar sarrafa man Gyada a 1943 a Maraɗi.
Show more...
1 month ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Ƙorafin makiyaya a Jigawa kan yadda ake saida filayen kiwo
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan wata matsala da ta kunno kai tsakanin makiyaya da manoma a yankin ƙananan hukuomin Guri da Kiri Kasamma da kuma Kaugama na jihar Jigawa a Arewacin Najeriya, inda Fulani makiyaya suka koka kan yadda aka salwantar da wuraren kiwon dabbobinsu da wurin shayar da su.
Show more...
1 month ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Yadda jihar Jigawa ta ɗauki matakin daƙile sare bishiyoyi barkatai
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ta'adar sare bishiyoyi barkatai ke tasamma karewar wasu bishiyoyi da ke da mutukar amfani ta fuskar tattalin arziki da kuma samar da kayan marmari, a gefe guda kuma hakan na barazana ga muhalli.
Show more...
1 month ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Yanayin ƙuncin da manoman masara a Tarayyar Najeriya suka shiga
Shirin namu na wannan mako zai yi duba ne kan yanayin ƙuncin da  manoman masara a Tarayyar Najeriya suka shiga a kasar, a dalilin tallafin rancen inganta noman masara da gwamnati ta basu ta hannun bankuna wanda ake kira Anchor borrowers.
Show more...
2 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Yadda damunar bana tazo da tasgaro ga manoma a wasu jihohin Arewacin Najeriya
A wannan makon, shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Micheal Kuduson  yayi duba ne kan yadda damunar bana tazo da tasgaro ga manoma a wasu daga cikin jihohin Arewacin Najeriya musamman jihar Kano duba da cewa har  zuwa wannan lokaci wasu ba su kai ga yin noma ba, ko kuma ba su jima da farawa ba.
Show more...
2 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Rashin fitar shuka ya zame wa wasu manoma ƙalubale a Jamhuriyar Nijar
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya tattauna a kan rashin fitar shuka a farkon daminar bana, lamarin da ya zame wa manoma ƙalubale babba a Jamhuriyar Nijar, matsalar da suka fara fuskanta tun daga farkon daminar bana.
Show more...
2 months ago
20 minutes 40 seconds

Muhallinka Rayuwarka
Yadda jihar Yobe ke ƙoƙarin rage rashin ayyukan yi tsakanin matasa ta hanyar habbaka noma
Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka na wannan makon zai yaɗa zango ne a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda duba da cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin jihar Yobe, inda kusan kashi 90% na al’ummar jihar ke harkar noma da kiwo.
Show more...
2 months ago
18 minutes 59 seconds

Muhallinka Rayuwarka
Illar da maganin ciyawa ke yiwa amfanin gona idan ba'a yi amfani da shi yadda ya dace ba
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya mayar da hankali ne kan illar da maganin ciyawa ke yiwa manoma, idan aka yi rashin sa'a ko kuma aka yi kuskure a yadda ya kamata a yi feshinsa.
Show more...
3 months ago
20 minutes 1 second

Muhallinka Rayuwarka
Tsadar takin zamani a Najeriya na barazana ga harkar noma a daminan bana
Shirin Muhalllinka Rayuwarka na wannan makon ya yi duba ne kan tsadar  takin zamani da ake samu Najeriya, lamarin da masana harkar noma ke cewa an kama hanyar fuskantar tsadar kayan abinci ko karancinsa.
Show more...
3 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Shirin gwamnatin Jigawa na farfado da noman yankin Sahara a jihar
Tun a karshen watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki, wato shekarar 2025, gwamnatin jihar Jigawa ta  kaddamar da shirin noman na yankin sahara karamar hukumar Maigatari dake masarautar Gumel. A  jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da shirin, gwamnan jihar, Umar Namadi ya ce an kirkiro shirin ne don bunkasa noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma rage kwararar mutane daga kauye zuwa birane.
Show more...
3 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a arewacin Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwa na wannan mako yayi duba ne kan yadda ake ƙara samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a yankin Arewacin Najeriya, yankin da hukumomi suka dade suna kiraye kiraye kan a rungumi harkar noman. Za mu kuma duba yadda hakan zai taimaka wa wadata ƙasa da abinci da kuma fa’idarsa ga muhalli.
Show more...
3 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Yunƙurin gwamnatin jihar Nasarawa a Najeriya na haɓaka noma da sarrafa rogo
A cikin shirin 'Muhalllinka Rayuwarka' na wannan makon, za mu yi duba ne akan yunkurin da gwamnatin jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya ke ta yi na habaƙa noma da sarrafa rogo. Mun ji daga mahukunta da manoman rogo a jihar, sai masana harkar noma da sauran masu ruwa da tsaki.
Show more...
4 months ago
19 minutes 40 seconds

Muhallinka Rayuwarka
Jigawa zata gina sabbin madatsun ruwa don bunƙasa noman rani
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin jihar Jigawa ta tarayyar Najeriya na gina sabbin ƙananan madatsun ruwa 10 a jihar domin bunƙasa harkar noman rani.
Show more...
4 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Halin da madatsun ruwa a jihohin Kano da Jigawa ke ciki kashi na 3
A wannan shirin za mu ƙarƙare jerin shirye-shiryen da muka fara kawo muku akan halin da madatsun ruwa ke ciki  jihohin Kano da Jigawa a Tarayyar Najeriya, da kuma yadda ya haan  ya shaf harkar noman rani da su, da kuma halin da ya jefa manoman da masunta, musamman ta fannin tattalin arzikinsu.
Show more...
4 months ago
20 minutes 1 second

Muhallinka Rayuwarka
Taron ƙasa da ƙasa ƙan nazarin ƙasar noma da kiwo a jihar Kano
Cibiyar nazarin da bincike kan ƙasar noma ta jam'iar Bayero a jihar Kano dake Najeriya ce ta shirya taron da ya hada ƙasashe da masana da suka yi duba a kai. Taron karo na biyar ya baiwa masana damar nazari don lalubo hanyoyin magance matsaloli da suka hadabi wannan sashe da ya hada da noma da kiwo a Sahel da wasu ƙasashen.
Show more...
5 months ago
20 minutes

Muhallinka Rayuwarka
Halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki?
A wannan makon, shirin zai yi duba ne kan halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki, da irin amfanuwa ko akasi da  masu cin moriyar su da suka haɗa da manoma da masunta da sauran al’ummmar yankunan ke yi da su.
Show more...
5 months ago
19 minutes 32 seconds

Muhallinka Rayuwarka

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).