Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin n...
All content for Daga Laraba is the property of Unknown and is served directly from their servers
with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.
Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin n...
Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin n...
Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki.
Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa. Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai...
Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya. Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa. A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa yunkurin kashe kansa har sau uku. ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ransa da kansa har sau uku?
Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027. A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu.
Wani sabon salo da wannan zamani ya zo da shi shi ne auren gwaji, inda mata kan yi shiga gidan miji da niyyar fita bayan wani lokaci. Sai dai manazarta suna cewa hakan ka iya haddasa matsalolin musamman idan mazajen auren ba su san da wannan shirin ba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu mata suke yin auren gwaji.
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.
A kokarin iyaye mata na kula da lafiyarsu da kuma tsare lafiyar iyalansu, hanyoyin bada tazarar haihuwa na asibiti sun zama zabin da dama ke komawa gare su. Sai dai duk da shaharar wadannan hanyoyi, akwai mata da dama da ke fuskantar matsaloli daban-daban yayin amfani da su. Wasu na fama da illa ta jiki kamar zubar jini fiye da kima, ciwon mara ko canjin yanayin jini, yayin da wasu kuma ke fama da matsaloli na tunani saboda tsoron illar hanyoyin ko rashin samun isasshen bayani d...
A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsalolin lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, na iya haifar da illa. Shiri...
Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta.
Wasu alummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi gwajin ma’aurata kafin a daura musu aure. A wasu lokutan akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure da suka hada da yaduwar cutuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi gwajin jini kafin aure.
A duk lokacin da akace an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abu na dabam da kuma basu damar shakuwa da ‘yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar masana harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata ace ana warewa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin hutun makar...
Masana da masu sharhi suna ganin cewa rasuwar shugaba Muhammadu Buhari ta haifar da babban gibi a siyasar Najeriya, musamman a Arewa. Wasu ma suna ganin rasuwar Buhari ka iya kawo tasgaro ga jamiyya mai Mulki, wadda take ganin shi danta ne, da ma sabuwar hadakar ’yan adawa, wadanda suke ganin yana tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan yadda siyasar Najeriya za ta kasance bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba.. Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da wasu suke ganin jajircewar mutum tana da nasaba da yawan abin da zai samu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan kujiba-kujibar da mutane suke yi don samun arziki da tambayar ko zafin nema yana kawo samu?
Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare. A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali. Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi nazari ne kan sinadaran da ake amfani da s...
Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya. Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya. Kazalika a kwanakin nan wani ...
An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin n...