Home
Categories
EXPLORE
True Crime
Comedy
Society & Culture
Business
Sports
History
Fiction
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
00:00 / 00:00
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts112/v4/56/e6/b4/56e6b4eb-2277-a0d3-4f63-5fb56c19027d/mza_6917202566084796642.jpg/600x600bb.jpg
Wasanni
RFI Hausa
24 episodes
Few seconds ago

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Show more...
Sports
RSS
All content for Wasanni is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Show more...
Sports
Episodes (20/24)
Wasanni
Karo na biyu a jere Alƙalan wasan Najeriya sun gaza samun wakilci a AFCON
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Najeriya ta gaza samun gurbin alƙalin wasanni a gasar AFCON karo na biyu a jere.
Show more...
3 days ago
9 minutes 54 seconds

Wasanni
Yadda Real Madrid ta doke Barcelona da ƙwallo 2 da 1 a haɗuwar El Classico
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya nazarci yadda aka yi fafatawa mai cike da armashi tsakanin Barcelona da Real Madrid wato haɗuwar hamayya tsakanin manyan ƙungiyoyin na Spain guda 2 karawar da ake kira El-Classico.
Show more...
1 week ago
10 minutes 1 second

Wasanni
An fara gasar Super Ligue ta Jamhuriyar Nijar
Shirin duniyar wasanni na wannan mako zai maida hankali a kan yanda aka fara gasar ligue ta ƙasar Niger da ake ma lakabi da SUPER LIGUE. A ƙarshen mako ne aka faro gasar Lik ta Jamhuriyar Nijar wacce ake wa laƙabi da Super Ligue.Ita dai wannan gasa ta Super League ta kasance kololuwar gasar kwallon ƙafa a ƙasar, inda ta ke ƙumshe da ƙungiyoyi 16,  kuma babban birnin ƙasar Niamey ka dai na da club 12.
Show more...
2 weeks ago
9 minutes 59 seconds

Wasanni
Makomar ƙasashen Najeriya, Senegal da Afrika ta Kudu a gasar cin kofin Duniya
Shirin a wannan mako ya mayar da hankali ne kan wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya ta 2026 da ƙasashen Amurka, Mexico da Canada za su karɓi baƙunci. A Nahiyar Afrika tuni dai wasu ƙasashe suka sami tikitin zuwa gasar da suka haɗar da Morocco da Tunisia da Aljeriya da Ivory Cost, sai dai ƙasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da kuma Senegal na cikin halin rashin tabbas, sai dai a wannan Talata ne za su san makomarsu.
Show more...
3 weeks ago
9 minutes 49 seconds

Wasanni
Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa ke baiwa ƙwallon Ƙafa a Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci za yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon Ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Najeriya.
Show more...
1 month ago
9 minutes 58 seconds

Wasanni
Mahangar masana game da yadda Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda ɗan wasan gaba na PSG ɗan Faransa Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana, bayan nasarar shi ta lashe kofuna da dama cikin kakar da ta gabata da ƙungiyar tasa da ke birnin Paris.
Show more...
1 month ago
10 minutes

Wasanni
Adawar magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙarawa gasar armashi
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan yadda adawar magoya bayan ƙungiyoyi ke karawa kwallon ƙafa tagomashi.
Show more...
1 month ago
10 minutes

Wasanni
Makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya
Shirin a wanan mako tare Khamis Saleh, ya yi duba ne kan makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya, inda a tsakiyar makon da ya gabata aka kammala wasannin na 8 na sharen fagen zuwa gasar lashe kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka za su karɓi bakunci a shekara mai zuwa. Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo.
Show more...
1 month ago
9 minutes 56 seconds

Wasanni
Yadda wasannin sharen fagen zuwa gasar cin kofin duniya ke gudana a Afrika
Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Tawagar ƙasar Morocco tuni ta samu nata tikitin bayan da ta haɗa maki 18, tazarar maki 8 tsakaninta da Tanzania. Tawagogin ƙasashe irinsu Masar da Algeria da Tunisia da Ghana da Afrika ta Kudu, duk da cewa akwai tazarar maki masu ɗan dama tsakaninsu da waɗanda ke mataki na biyu a rukunansu, har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Show more...
1 month ago
10 minutes

Wasanni
Yadda ake samun takun saƙa tsakanin ƙungiyoyi da 'yan wasa wajen canza sheƙa
Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan yadda ake samun takun saƙa tsakanin ƴan wasa da ƙungiyoyinsu a duk lokacin da suke son sauya sheƙa. A duk lokacin da a ka buɗe kasuwar sayen ƴan wasa a duniya, a kan samu takaddama lokaci zuwa lokaci tsakanin ƴan wasa da kuma ƙungiyoyin su saboda wasu ƙungiyoyi na kin amincewa da ƴan wasansu su sauya sheka lokacin da su kuma ƴan wasan ke son bari.
Show more...
2 months ago
10 minutes

Wasanni
Sabon jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees na ƙoƙarin farfaɗo da martabarta
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya yi dubu ne kan amsar ragamar jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees da ke jihar Kaduna a Najeriya, da ɗan wasan Super Eagles Sadiq Umar Jololo da kuma ɗan majalisar wakilai Hon. Bello El-Rufai suka yi.
Show more...
2 months ago
9 minutes 59 seconds

Wasanni
Yadda wasanni suka gudana bayan fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a Turai
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya mayar da hankali ne a kan yadda aka fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a bana a manyan Lig-Lig na sassan nahiyar Turai.
Show more...
2 months ago
10 minutes

Wasanni
Yadda wasanni ke ɗaukar hankalin matasa a lokacin hutu a Nijar
Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan yanda wasanni ke ɗaukan hankalin matasa a irin wannan lokaci na hutun ƴan makaranta a Nijar.
Show more...
2 months ago
9 minutes 59 seconds

Wasanni
Yadda shugaban Najeriya ya tarbi tawagar Super Falcons bayan lashe gasar WAFCON
Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan karramawar da gwamnatin Najeriya ta yi wa tawagar Super Falcons na lashe gasar WAFCON.
Show more...
3 months ago
9 minutes 43 seconds

Wasanni
Yadda ta kaya a gasar lashe kofin Afirka ta mata
Shirin Duniyar Wasanni  a wannan makon tareda Khamis Saley  yayi  duba ne kan wasan ƙarshe na gasar lashe kofin mata ta Afrika WAFCON da aka yi a ƙarshen mako.
Show more...
3 months ago
9 minutes 59 seconds

Wasanni
Yadda RFI hausa Hausa ta ƙulla alaƙa da ƙano pillars
a cikin shirin Duniyar wasanni na yau zaku ji yadda sashin Hausa na RFI ya ƙulla yarjejeniyar Naira miliyan 100 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars dake Arewacin Najeriya a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2025. A latsa alamar sauti domin domin sauraren cikakken shirin.
Show more...
3 months ago
9 minutes 54 seconds

Wasanni
Tasirin wasannin sada zumunta ga manyan ƴan wasa a lokacin hutun manyan Lig
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mayar da hankali kan wasanni da ke gudana a lokacin hutu, ta yadda manyan ƴan wasa daga lig lig na Turai da sauran nahiyoyi ke komawa gida don doka wasannin sada zumunta a irin wannan lokaci, lamarin da ke nishaɗantarwa da kuma ƙara danƙon alaƙa tsakanin manyan ƴan wasan da masu tasowa.
Show more...
4 months ago
10 minutes

Wasanni
Kwara da Rivers sun lashe kofin ƙalubale na Najeriya a bangaren Mata da Maza
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali ne kan wasannin ƙarshe na gasar cin kofin ƙalubale na Najeriya, wadda yanzu ake kira President Federation Cup, da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke birnin Lagos.
Show more...
4 months ago
9 minutes 59 seconds

Wasanni
Shirye-shiryen sun yi nisa na fara gasar Firimiyar Najeriya ta baɗi
Shirin Duniyar Wasanni a wanan mako ya yi dubu ne kan shirye-shiryen fara gasar Firimiyar Najeriya ta kaka mai zuwa, kuma tuni hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato NPFL, ta sanya 22 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar soma kaka ta baɗi. An dai ji shugaban hukumar shirya babbar gasar ta Najeriya Gbenga Elegbeleye na cewar, suna duba yuwuwar soma amfani da na’urar VAR a gasar mai zuwa, baya ga kuma inganta kayayyakin gudanarwa.
Show more...
4 months ago
10 minutes

Wasanni
An bude gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi a Amurka
Shirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana. 
Show more...
4 months ago
9 minutes 30 seconds

Wasanni

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.