An samu wani da ya ke ganin ya fi Annabi ilimi da iya adalci, don haka ba abin mamaki ba ne ko yaushe kuma a ko ina, a samu wasu da suke ganin ilimin su ya kai matsayin da hatta Malaman su, ba su ganin su da gashi a ido.
Malamai da suka wallafa littafai a baya, sun duba yanayin al'umarsu ne da buqatuwar al'umar tasu ga wannan littafai da suka rubuta, shi ya sa suka wallafa su.
Misali idan ka duba irin su Aqida Wasitiyyah, Aqida Hamawiyyah da su Tadmuriyyah, ai duk daga sunayen garuruwa ne aka basu suna, Ibn Taymiyyah ya wallafa su ne musamman ga mutanen wadannan wurare.
Shin laifi ne in kwaikwayi wani?
Akwai wasu sinfin mutane da Shari'a ta yadda in kwaikwaya ne?
Mun tattauwa akan wannan mas'ala ganin cewa musamman matasan, suna duba zuwa ga wasu mutana ne suna kwaikwayon irin rayuwar su.
Wannan ne karo na farko da muka tattauna da macce. Ganin cewa wantan Azumi ya kama, mata da yawa suna dukufa wajen aikin neman Aljanna ta hanyar hidima da gida, miji, yara da kuma babban abin, wato Ibada. Shin wai wadannan
matan, ya ya suke yi ne ganin cewa kema Allah Ya azurta ta da aure, yarinya kuma tana kasuwancin ta?
Ku saurari tattaunawar mu da Fatima Zarah Maitambari
Yadda watan Ramadan ya gabato, yana da kyau a ce mutum ya gama duk wata shiri da ya ke tunanin ya yi yanzu. A wannan tattaunawar, mu yi magana kan wani muhimmin abu da ya kamata a ce mu sani game da Rayuwar mu da kuma Ramadan
Musulmi mun zama mutane da sai abu ya faru sannan muke neman daukar mataki. Haka kuma na nuna rashin wayewa ne da kuma ci baya. Kamata ya yi a ce kafin abu ya faru, mun riga mun tanada abubuwa da za su tinkari abin. In alheri, alheri in kuma sharri, rigakafi.
Wannan tattunawar ta kawo fukoki fuda biyu da suka kamata ace muna amfani da su.
Allah bamu iko gyarawa, amin.
Ayi sauraro lafiya.
Mun tattauna yadda al'amura suke yanzu musamman kasancewar lokaci ne na zabe. Shin wai me ya kamata mu yi a matsayin mu na Musulmi? Ina muka dosa sannan gaba wace irin shiri zamu yi ne?
Saurara ku ji hirar ta mu.